Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni ya bai wa ƴaƴan Sheikh Goni Aisami aikin yi, malamin da wasu sojoji su ka yi masa kisan gilla a jihar.

Gwamna Buni ya bayar da izinin ɗaukarsu aikin gwamnati ne a jiya Talata a yayin ziyarar da iyalan Malamin su ka kai masa.

Biyu daga cikin ‘yan Malamin gwamnan ya bayar da umarnin da a dauke su aikin.

Gwamnan ya kuma bayyana musu cewa gwamnatin sa za ta tsaya don ganin a binciki lamarin yadda ya kamata.

Gwamna Buni ya kuma bayyana musu cewa gwamnatin za ta ci gaba da tallafa musu a al’amuransu na yau da kullum.

Malam Ibrahim Aisami daya daga cikin wadanda su ka ziyarci gwamnan ya yi magana a madadin ‘yan uwa ya mika godiyarsu bisa ta’aziyyar da gwamnan ya tura tare da aikewa da tawagar mutane daga fadarsa domin yin ta’aziyyar ga iyalan marigayin.

Ya kara da cewa aikin da gwamnan ya bai wa ‘yanƴan Malamin zai rage musu radadin halin da su ke ciki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: