An bude ofishin jam’iyyar NNPP na jihar Borno kwana daya bayan garkameshi da aka yi ranar Laraba.

Saifullahi Hassan, mai magana da yawun dan takarar shugaban kasa karkashin jam’yyar, Rabiu Musa Kwankwaso, ya sanar da hakan a shafinsa na Tuwita.

Hassan yace bayan haka gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bada hakuri bisa abinda ya faru.

Jami’an tsaro dauke da bindigu da ake zargin yan sanda ne, a safiyar ranar Alhamis sun mamaye sakatariyar jam’iyyar NNPP da ke Maiduguri, Jihar Borno kwanaki kadan kafin kaddamar da ofishin da ke kusa da Abbaganaram.

Majiyoyi sun ce rikicin ya samo asali ne a ranar Laraba bayan da shugabannin jam’iyyar suka dauki hayar leburori su musu fentin sabuwar sakatariyar, gabanin zuwan dan takarar shugaban kasarsu, Rabiu Kwankwaso don kaddamar da ofishin.

Amma, wasu da ake zargin yan daba ne daga jam’iyyun hamayya suka kutsa sakateriyar suka lika fastocin yan takarar su a wurare daban-daban a harabar sakateriyar.

Kwankwaso a cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis, 25 ga watan Agusta, tsohon gwamnan na Jihar Kano ya yi Allah-wadai da matakin.

Amma, duk da hakan ya yi kira ga magoya bayan jam’iyyarsu ta NNPP su kwantar da hankulansu tare da kasancewa masu bin doka da oda a yayin da suke kokarin warware matsalar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: