Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da cewa jami’nta sun samu nasarar kama wani kasurgumin dan bindiga mai suna Isyaku Babangida wanda rundunar ta dade ta na nema.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Muhammad Shehu ne ya sanar da kama dan bindigan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya juma’a.

Sanarwar kakakin ta bayyana cewa an kama kasurgumin dan bindigan a yayin wani bincike da jami’an su ka gudanar a kananan hukumomin Bukuyum da Anka na Jihar.

Muhammad Shehu ya kara da cewa sun kama Isyaku ne da tallafin bayanan sirri da su ka samu a lokacin da wata tawagar ‘yan bindiga karkashin jagorancin Alhaji Bello su ke yunkurin kai hare-hare wasu garuruwa da ke kananan hukumomin na Anka da Bukuyum.

Kakakin ya ce bayan samun bayan su ka aike da jami’an su inda su ka tarar da wani sansanin ‘yan bindigan harta kai ga sun yi musayar wuta.

Ya ce bayan bude musu wuta da jami’an na ‘yan sandan su ka yi hakan ya tilasta musu tserewa tare da jikkata su.

Shehu ya ce daga nan ne jami’n su ka samu nasarar kama dan bindigan da rundunar ta dade ta na nem na kauyen Kabe da ke Jihar Kebbi.

Kakakin ya bayyana cewa ‘yan sandan sun kwato bindiga kirar AK47 da harsasai.

Shehu ya ce bayan kama dan bindinga ya bayyana musu yadda su ke kai hare-hare kauyukan Bukuyum Anka da kuma Gummi tare da yin garkuwa da mutane da dabbobinsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: