Kungiyar kwallon kafa ta gidajen gyaran hali ta Kasa reshen Jihar Kano wato (Kano Correctional Tigers) ta fitar da sanarwar kira ga dukkan ‘yan wasan kungiyar da su ci gaba da zage damtse wajen fitowa daukar horo kamar yadda ta saba a kowanne lokaci.

Kiran na zuwa ne ta bakin shugabannin kungiyar ta kwallon kafa ta gidajen gyaran halin da ke Jihar ta Kano.
Shugabanin sun bayyana cewa kungiyar na daf da shiga babbar gasar da ake shirin fara wa ta jami’an tsaron da ke Jihar ta Kano.

Kungiyar ta kuma ta ya murna ga sabon Kocin kungiyar da aka nada mai suna Pele Gwale tare da fatan samun nasara a yayin fara aikin.

Sanarwa hakan na zuwa ne a yau Asabar ta bakin Kaftin din Kungiyar ta gidajen gyaran hali ta kasa reshen Jihar ta Kano wato
AIC Abbas Abubakar musa.