Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Jihar Legas LASEMA ta tabbatar da mutuwar wasu fasinjoji yayin wani hadari da su ka yi a Jihar.

Hadarin ya farune a yammacin jiya Lahadi inda motar ta ke dauke da mutane 14 ta kife.

Hukumar ta ce motar wanda ƙirar Bas ce, ta kama da wuta ne a lokacin da ta ke tsaka da tafiya.

Jami’an hukumar sun bayyana cewa motar fasinjojin ta na dauke ne da lambar garin Ikeja da ke Jihar.

LASEMA ta bayyana cewa hadarin ya farune sakamakon tukin ganganci da gudun wuce sa’a da direban motar ke.

Sakataren din-din-din na hukumar ta LASEMA Dr Olufemi Oke-Osanyintolu ya ce direban motar ya tsira daga hadarin.

Dr Olufemi ya kara da cewa a yayin hadarin an kubutar da mata uku da namiji daya kuma an kai su Asibiti.

Sakataren ya ce mutane bakwai ne su ka rasa rayukansu ciki harda wani karamin yaro a lokacin da su ka kone kurmus.

Dr Oke ya ce bayan faruwar lamarin sun tattara gawarwakin mutanen zuwa Asbiti.

Leave a Reply

%d bloggers like this: