Gwamnatin jihar Zamfara ta buɗe makarantu 45 daga cikin 75 da ta rufe a jihar

Gwamnatin ta rufe makarantun a baya bisa ƙalubalen tsaro da kuma barazanar sace ɗalibai da ƴan bindiga ke yi.

Ma’aikatar ilimi a jihar ta tabbatar da sake buɗe makarantu 45 daga cikin 75 da aka rufe kamar yadda babban sakatare a ma’aikatar Alhaji Kabiru Attahiru ya tabbatar.

Tun a watan Satumban shekarar 2021 aka rufe makarantun da ka iya fuskantar matsalar tsaro bayan da aka sace ɗalibai a makarantar Ƙaya da ke ƙaramar hukumar Maradun ta jihar.

Gwamnatin ta raba launin kayan makaranta zuwa launi uku, daga ciki akwai Ja, Shuɗi da ruwan ɗorawa.

Ya ce ma’anar rarraba launin kayan, Ja an yi wa ɗaliban makarantar da yankunansu su ke tsanananin matsalar tsaro, sai ruwan ɗorawa wanda yankunansu ke matsakaicin fuskantar matsalar sannan shuɗi a makarantun da ba a fuskantar matsalar tsaro a yankunan.

A cewar sakatare a hukumar ilimi ta jihar, buɗe makarantun ya biyo bayan samun zaman lafiya a jihar.

Kuma zuwa nan gaba kaɗan za a buɗe sauran makarantun da su ka rage a rufe.

Jihar Zamfara ta shiga tsananin matsalar tsaro daga masu garkuwa da mutane, ƴan fashin daji da sauran ayyukan ta’addanci.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: