A yau Alhamis ne aka sake gurfarnar da dan asalin kasar China mai suna Frank Geng mai shekaru 47, a gaban babbar kotun jiha bisa zargin kisan budurwarsa ‘yar Najeriya.

A na zargin ɗan ƙasar China da hallaka Ummukulsum Sani wadda akafi sani da ummita.
Ana tuhumar Frank mazaunin anguwar railway, da laifin kisan kai.

A ranar 4 ga watan oktoba ne kotun ta umarci gwamnatin Kano da ta samawa Frank tafinta.

Da aka sake gurfanar da shi a yau, lauyan gwamnati Musa Abdullahi Lawan ya gabatar da Guo cumru daga ofishin jakadancin China domin ya yi wa wanda ake kara tafinta.
An shaidawa kotun cewa wanda ake karar ya aikata laifin ne a ranar 16 ga watan Satumba, a anguwar Jambulo dake yankin karamar hukumar Gwale a Kano.
Mai gabatar da karar ya karanto zargi cewa a ranar ne da misalin karfe tara na dare ɗan ƙasar China ya yi amfani da wuƙa wajen hallaka budurwasa.
Sai dai wanda ake zargin ya musanta zargin da ake masa.
Kasancewar laifin da ake zargin dan Chinan ya sa6a da sashe 221 (B) na dokar laifuka ta kano.
Alkalin kotun Sunusi Ado Ma’aji ya bayar da umarnin ajiye wanda ake kara a gidan gyaran hali har zuwa ranar 16 ga watan Nuwamba mai kamawa.