Wata babbar kotun tarayya ta haramtawa jam’iyyar PDP tsayar da dan gwamnan jihar Zamfara a zaben shekarar 2023.

A yau Talata ne alkalin kotun da ke zamanta a Gusau, mai shari’a Aminu Baffa ya yanke hukuncin tare da soke sabon zaben dan takarar gwamnan da PDP ta gudanar.
Jam’iyyar PDP ta gudanar da sabon zaben dan takarar, wanda Dauda Lawal Dare ya lashe ne, bisa umarnin kotun na watan Satumba.
Rikici ya kunno kai a jam’iyar PDP tun bayan da Dauda Lawal Dare ya lashe zaben da jam’iyar ta gudanar a ranar 25 ga watan mayu da kuri’a 431.

Sauran ‘yan takarar uku Abubakar Nakwada, Wadatau Madawaki da Ibrahim Shehu Gusau, sun janye daga zaben bisa zargin magudi, saidai baturen zaben Adamu Maina yayi watsi da janyewar tasu saboda basu sanar a hukumance ba a cewarsa.

Amma a watan Yuni sauran ‘yan takarar Shehu Gusau Madawaki da Hafiz Muhammad su ka shigar da kara suna kalubalantar sakamakon zaben wanda Dauda Lawan ya lashe, don haka suka bukaci kotu ta soke shi saboda kura-kurai da saba dokar zabe da kuma magudi da sukace an tafka.
A watan Satumba alkalin kotun mai shari’a Aminu Baffa ya amsa bukatarsu tare da soke zaben na farko, kana ya bayar da umarnin gudanar da sabon zabe, wanda bayan an gudanar Dauda Lawan Dare ya sake lashewa.
Sai dai kuma a zaman kotun na yau, kotun ta soke nasarar da Dauda Lawan Dare tare da bayyana cewa jam’iyar PDP bazata shiga zaben gwamna ba a jihar na shekarar 2023