Kungiyar ASUU ta malaman jami’a a Najeriya tana shirin yin zanga-zangar lumuna a fadin Najeriya domin nunawa gwamnatin kasar fushinta.

Punch ta kawo rahoton da ya nuna cewa malaman jami’an za suyi zanga-zanga na kwana guda saboda rashin hana su albashi da gwamnatin tarayya tayi.

Gwamnatin tarayya ta dauki tsarin ‘babu aiki-babu albashi’ ga malaman da suka shiga yajin-aiki, matakin ya fusata ‘ya ‘yan kungiyar ASUU.

Za a gudanar da wannan zanga-zanga ne a jami’o’in gwamnati da ke jihohin kasar nan .

Ana sa ran a ga malaman da ke cikin kungiyar sun hau tituna daban daban.

Hakan yana nufin a ranar da za ayi wannan zanga-zanga ta lumuna, ba za a koyar da dalibai ba, babu malamin jami’ar da zai shiga aji domin bada darasi.

Wani ‘dan majalisar koli watau NEC ta kungiyar ASUU, ya shaidawa Punch wannan a lokacin da ya zanta da manema labarai a ranar Lahadin da ta wuce.

Malamin jami’ar yake cewa kowace makaranta za ta tsaida ranar da za tayi na ta zanga-zangar, ba a lokaci daya za a kaure da zanga-zangar a Najeriya ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: