Jam’iyyar PDP ta ce kuskuran da dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya yi a wajen kaddamar da takararsa a Jihar Filato, kan nemawa PDP albarka a maimakon APC, wata alama ce ta nasara, PDP ta ce wannan wata ‘yar manuniya ce ta cewa jam’iyyar ce za ta yi nasara a babban zabe mai zuwa na shekarar 2023.

Sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa, Debo Ologunagba ne, ya bayyana hakan a ranar Talata, inda ya ce nasara na tare da su ba jam’iyya mai mulki ba.
Hakazalika, ya ce yana da kyau APC ta fahimci cewar ‘yan Nijeriya ba sa muradin sauraren dukkan wani jawabi daga bakin dan takararta, Inda yace dan takarar APC ya fi kyau ya mayar da hankali kan bayanan bogi da ya bayar wanda suka shafi iliminsa, shekaru da kuma tarin aikin da ya yi ga ‘yan Nijeriya a yanzu.

Jam’iyyar ta PDP ta kara dacewa, addu’a wata alama ce ta nasara, wanda Asiwaju Tinubu da yana da kwarin guiwa da ya nemi gafarar ‘yan Nijeriya ya hakura da neman takara,” kamar yadda ya bayyana.

A jiyane dai dan takarar Shugabancin ƙasa na jam’iyyar APC Bola Ahmad Tinubu yayi kuskuran ambatar jam’iyyar PDP a maimakon sunan jam’iyyar sa wajen nema mata albarka, yayi gabatar da yakin neman zabensa a jihar Filato.