Tsohon Shugaban kasar tarayyar Najeriya Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa, hatsaniyar da take faruwa tsakanin kungiyar Malaman Jami’o’i da gwamnatin tarayya bata da ranar karewa.

Ya kuma bayyana cewa ko shi a lokacin gwamnatinsa ya samu matsala da kungiyar malaman jami’o’in, duk kuwa da kokarinsa da ganin ya wadatar dasu.
Ya bayyana hakan ne ya wajen taron kolin ilimin manyan makarantu Na kwanaki biyu a Abuja, wanda ofishin kakakin majalissar wakilai Femi Gbajabiamila ya shirya.

Ya kuma yabawa kakakin majalissar ta wakilai bisa kokarinsa na shiga tsakanin rikicin, wanda hakan ya zamo silar janyewar yajin aikin na tsawon watanni takwas.

Jaridar Punch ta ruwaito Obasanjo yana cewa, Ilimin manyan makarantu Abu ne mai muhimmanci amma zai karfafi ilimin ne gaba daya na kowanne bangare.
Obasanjo ya kara da cewa a lokacin da yana mulkin kasar nan hakan ta faru tsakanin sa da ASUU, bayan da aka biya musu bukatun sai suka fara sayen motoci da gina Gidaje. Har Malaman Firamare saida suka sayi motoci.
Ya kara da cewa, dole kasar nan ta samar da ilimi ga yara miliyan Ashirin da basa zuwa makarantu, Dan gudun sake afkuwar samar da ‘Yan kungiyar Boko Haram.