Majalissar Dattijai tayi sammacin Ministan kudin tarayyar Najeriya Zainab Shamsuna Ahmad, Dan tayi musu bayanin akan kudi Kimanin Naira Biliyan 206 da aka sa acikin kasafin kudin shekara 2023 na ma’akatar Jin kai da kula da walwalar Al’umma.

Kwamitin Ayyuka na musamman na majalissar Dattijan sun bukaci Ministan da tazo tayi musu bayani, akan wadannan makudan kudaden da aka sa duk da halin karancin haraji da matsin tattalin Arziki da Kasar ke fama da shi a wannan lokacin.
Jaridar Premium Times ta ruwaito cews bukatar gayyatar ministan ta samo asali ne, a lokacin kare kasafin kudin ma’aikatar jin kai da kula da walwalar Al’umma.

Biyo bayan kasa sahihin bayani da ministar ma”aikatar Sadiya Umar Faruq tayi akan kudaden, Sadiya ta bayyana cewa bata san ta yaya akayi ma’akatar kudin ta saka kudaden a cikin kasafin kudin ma’akatarta na shekara mai kamawa ba.

Ta bayyana cewa kuma, ma’akatarta ta bukaci wasu kudade a wannan shekarar da muke ciki Dan yin wasu Ayyuka a hukumar cigaban yankin Arewa maso Gabas.
Saidai ta bayyana cewa bata saki kudaden ba a lokacin, amma yanzu tayi mamakin ganin kudin har ninki goma acikin kasafin kudin ma’akatarta na shekara mai zuwa.
Memba acikin kwamitin sauraran bayanan kasafin kudin Elisha Abbo yayi ikirarin cewa, akwai bukatar su gayyato Minista Zainab Dan tayi musu bayanin yadda aka sanya kudaden.
Inda yace sun gano kudi kimanin Biliyan 301 wanda za’a biyasu ta hanyar ciyo bashi mabanbanta, kuma sun tambayi ministan da tayi musu bayani akan ayyukan da za’ayi dasu.
Saidai ya kara da cewa, Sadiya ta gaza yi musu jawabi akai, tace bata san dasu ba saidai a tambayi ministar kudi Zainab Ahmad Shamsuna.