Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta dora alhakin talauci da matsin rayuwa da yan Najeriya ke ciki a kan gwamnonin jihohi.

Karamin ministan kasafin kudi da tsare-tsare, Clem Agba ne ya bayyana hakan ga manema labarai bayan taron majalisar zartarwa na tarayya a yau Laraba.

Ya ce shirin gwamnatin tarayya na kyautata rayuwar yan kasar bai yi tasirin da yakamata ba saboda gwamnonin jihohin ba su bai wa gwamnatin tarayya hadin kai ba.

Mr Agba ya kara da cewa gwamnonin sun fi mayar da hankali wajen aiwatar da ayyukan da ba su da muhimmanci, maimakon inganta rayuwar al’ummar karkara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: