Kakakin Yaɗa Labaran yakin neman zaben ɗan takarar shugaban kasa na ja’iiyyar APC ya tabbatar da cewa ɗan takarar su bai taɓa ɗaura niyya ba ballantana bayyana cewa idan ya ci zaɓe zai ɗauke birnin tarayya daga Abuja ya mai da shi jihar Legas.

Bayo Onanuga ya ce wannan magana ƙarairayi ne, da sharri kuma yarfen ‘yan jamiyyn PDP da LP ne.

Ya ce ya yi mamakin yadda wasu dattawa da ya yi iƙirarin cewa PDP ce ke biyan su kuɗaɗe su na yaɗa ƙarairayi, za su riƙa kitsa maganganun da ba su da tushe ballantana makama.

An dai ƙirƙiro Babban Birnin Tarayya Abuja cikin shekarar 1976, a ƙarƙashin gwamnatin mulkin soja ta marigayi Janar Murtala Mohammed, sai dai kuma an baro jihar Legas ne aka koma Abuja a cikin 1991, ƙarƙashin mulkin Janar Ibrahim Babangida mai ritaya.

Onanuga ya ce ya kamata duk mai hankali ya gane cewa babu yadda za a yi Tinubu ya yi tunani ko mafarkin cewa zai mai da babban birnin tarayya zuwa Legas.
Tinubu dai ya na ci gaba da shan suka ta adawa da matsin lamba daga fuskoki daban-daban.

Babban matsin lambar da ya fi fuskanta ita ce takarar Musulmi da Musulmi, wadda wasu Kiristoci su ka ce ba za su taɓa jefa masa ƙuri’un su ba.

Sannan kuma akwai batun cewa matar sa da ‘ya’yan sa duk Kiristoci ne, wanda hakan ya fara janyo masa koma-baya a Arewa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: