Dan takarar Jam’iyya mai mulki ta APC Asiwaju Bola Tinubu ya bayyana cewa, ba zai bawa shugaban kasa Muhammadu Buhari kunya ba idan aka zabe shi a matsayin shugban kasa a zabe mai zuwa.

Tinubun ya bayyana hakan ne a wajen wata kebantacciyar walimar cin abinci, wacce iyalai da makusantan Shugaba Buhari suka shirya na bikin murnar cikarsa shekaru 80 a Duniya.
Jaridar Vanguard ta ruwaito an yiwa walimar take ne da cewa “Taya murna ga Dan kishin kasa, Shugaba kuma Dattijon Kasa.”

Dan takarar na jam’iyyar APC kuma yayi godiya ga Shugaba Buhari, sakamakon sadaukarwarsa na ganin cigaban Najeriya.

Kuma ya bayyana cewa Buhari ya karbi Shugabancin kasarnan a lokacin matsi, kuma sun ga sadaukarwarsa da kishin kasa hadi da gaskiya. Yayi kokari kuma yan kasa sun ga irin shugabancin da ya wanzar.
Tinubu ya kuma cewa, sun kasance cikin shugabannin da suka zo Dan bautawa kasarsu, cikin sadaukarwar, kishin kasa da kuma gaskiya.
A karshe ya kwatanta Shugaba Buhari da shugabanni irin su Charles De Gaulle na Faransa, Franklin Roosevelt na Amurka da kuma Winston Churchill na Birtaniya.