Ma’aikatar aikin hajji ta kasar Saudiyya ta fara yiwa maniyya aikin hajjin bana na shekarar 2023 rijistar a ranar Alhamis.

Bayan bude rijistar da Ma’aikatar ta yi ta ce wajibi ne dukkan wani maniyyaci sai ya kammala yin riga kafin cutar korona tun saura kwana goma kafin ranakun fara aikin hajji.
Hakan na zuwa ne kwanaki kalilan da ma’aikatar ta bayyana hukumar aikin hajji ta Najeriya NAHCON cewa ta dakatar da kammala daukar allurar riga kafin cutar korona ga maniyyata.

Kamfanin dillancin labaran kasar saudiyya SPA ya rawaito cewa gwamnatin kasar ta saudiyya ta jadda soke tafiya da muharrami namiji ga mata maniyya aikin hajji.

SPA ta ce ma’aikatar ta kuma bude sabon tsarin adashin gata ga duk wani maniyyacin kasar masu karamin karfi akan riyal 3,984.
A sabon tsarin adashin gatan da ma’aikatar ta bude ga masu karamin karfi za su iya biya sau uku domin samun damar kammala biyan kudin.
Ma’aikatar ta bayyana cewa daga cikin shekarun masu yin rijistar takafar Intanet za su fara ne daga shekara 12.
Ma’aikatar ta kara da cewa a wannan shekarar ta 2023 za ta fi bai wa maniyyatan shekarar 2022 kujerun da ba su samu damar zuwa ba.
Ma’aikatar ta kuma yi kira ga maniyya da su tabbatar sun yi rijistar a kamfanoni masu lasisi domin kaucewa fadawa hannun ‘yan damfara.