Wasu ‘yan banga a garin Zuba da ke babban birnin tarayya Abuja, sun kama wani da ake zargi mai suna Bello Yellow, da ke da alaka da harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.

An kama wanda ake zargin ne da sanyin safiyar Lahadi lokacin da ya taso daga motar da ke kusa da tashar Motar Dan-Kogi.
Wani daga cikin dan banga ya ce ‘yan banga na kungiyar Miyetti Allah ne suka ga wanda ake zargin.

Ya ce, sun jawo hankalin mambobinsu da ke wurin dajin don neman taimako.

An kama shi aka kai shi ofishinsu inda aka bincike shi aka tsare shi kafin a mika shi ga ‘yan sanda da misalin karfe 4 na safe.
Majiyar ta bayyana cewa a yayin binciken an gano tsabar kudi N103,000 a hannun sa, da kuma sandunan sigari guda uku da abin kunnata.
Majiyar ‘yan bangan ta bayyana cewa jami’in ‘yan sandan shiyya na Zuba da kan sa ya zo ofishinsu tare da mutanensa domin daukar wanda ake zargin.
Ya kara da cewa, duk da cewa ’yan bangar Fulani sun bayyana sunan wanda ake zargin da Bello Yellow, amma ya kira kansa da Bature Shabe, kuma ya fito daga Ilorin a Jihar Kwara yana kan hanyarsa ta zuwa dajin Shenagu kusa da Zuba inda babban yayansa, Alhaji Shabe yake zaune.