Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da sabon taken Jihar Kano domin inganta kishin Jihar a tsakanin alumma da ke cikinta.

Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwaman Abba Anwar ya fitar a ranar Lahadi.
Sakataren ya ce gwamantin ta yi hakan ne domin ganin ta adana tarihi da al’ada domin ci gaban Jihar.

Sabon Taken jihar Kano da gwamnatin ta kaddamar ya kasance ne a harshen Hausa inda aka gudanar da shi a fadar gwamnatin Jihar.

A yayin taron gwaman ya yabawa matar sa Hajiya Hafsa Ganduje wanda ta bayar da gudummawa wajen assasa Taken.
Sanarwar ta ce daga bisani gwamnatin za ta aike da taken gaban majalisar Dokokin Jihar domin ya zama doka.