Dan takarar shugaban kasa a Jam’iyyar NNPP Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa sauyin fasalin kudin da bankin CBN yayi akwai babban kuskure a cikisa.

Dan takarar ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a, inda ya ce lokacin da aka sauya fasalin kudin bai dace ba wanda hakan ya kara jefa ‘yan Najeriya cikin Talauci.
A yayin wata hira da aka yi dashi a gidan Talabijin na Channels kwankwaso ya yi alkawarin kara wa’adin karbar tsofaffin kudaden idan ya zama shugaban kasa har zuwa lokacin da mutanen kasar sabon kudin zai wadata a hannun su ba tare da wata matsala ba.

Sanata kwankwaso ya bayyana cewa baya goyon bayan sauyin fasalin kudin, musamman a lokacin da ya ke gabatowa ana bukatar zaman lafiya domin ganin an tabbatar da anyi sahihin zabe cikin kwanciyar hankali da ci gaba ta yadda mutane za su zabi wanda su ke so.

Kwankwaso ya kara da cewa tun bayan sauya fasalin sun yi kira da ya tsawaita wa’adin wanda hakan ya sanya aka kara kwanaki goma wanda shima hakan bazai kawo canji ba.
Kazalika sauyin da CBN yayi yayi shi ne a lokacin da bai kamata ba sannan kuma bai yi tanade-tanaden da su ka dace ba kafin sauya kudin.