Hukumar tsaron farin Kaya ta DSS ta gayyaci daraktan yada labarai na kafafen sada zumanta na dan takarar jamiyar APC Bola Ahmad Tunubu wato Fani Kayode bisa tuhumarsa kan furucin da yayi na cewa ana kokarin juyin mulki a Najeriya.

Kayode ya bayyana cewa ya samu gayyata daga hukumar farin Kaya ta DSS a shafinsa na Twitter a safiyar yau litinin.
Kuma zai amsa kiran da hukumar ta farin kaya DSS ta masa.

Sannan ya ci gaba da cewa zai fadi gaskiya bisa abubuwan da ya sani game da kasar da kuma ra’ayin sa in har yana raye, don kuwa babu wani abu daya ke jin tsoro.

A ranar Asabar din karshen makon da ya gabata ne cikin wani sakonni dake yawo a kafafen sada zumunta daga Kayode ya ce ya fahimci cewa Dan tankarar jamiyar PDP Atiku Abubakar yayi wata ganawa da manyan sojin ƙasar.
Sai dai bisa fitar wannan batu helkwatar tsaro ta soja sun musanta batun Fani Kayode inda ta ce tana ci gaba da kare damakwaradiyya.