Yan sanda a kasar Uganda sun tabbatar da kama wani maaikacin jinya da ake zargin da yiwa wasu mata biyu masu dauke da juna biyu fyade a babban Asibitin gwamnatin kasar ta Uganda.

Kamar yadda mataimakin jamin hulda da jama a na hukumar yan sanda mai suna Luke ya bayyana ga manema labarai a yau Litinin.

Ya ce lamarin ya faru ne a jiya Lahadi a babban birnin kamfala na kasar Uganda.

An kama wani mai suna Kutesa Denis an a bisa zargin yiwa wasu mata biyu fyade wadanda suke dauke da juna biyu a Asibitin Entebbe a Uganda.

Ya ci gaba da cewa ana zargin mutumin da baiwa matan biyu miyagun kwayoyi kafin yi musu aika aikar.

Kuma bayan binceke da yan sanda suka aiwatar a gidansa an gano wasu kwayoyin a tare da shi da wata wasika.

Sannan hakan ya sa wasu da yawa daga cikin mata su ka fito sun bayyana cewa anci musu zarafin.

Shi ma shugaban Asibitin gwamnatin Entebbe Peterson ya bayyana cewa za a ci gaba sanya kula da kuma sanya kyamarorin tsaro a ciki da waje na Asibitin domin samar da cikkaken tsaro.

Leave a Reply

%d bloggers like this: