Sunan dan takarar sanatan Kano ta tsakiya na jam’iyyar NNPP Rufa’i Sani Hanga, yayi batan dabo a jerin sunayen karshe da INEC ta fitar na yan takarkaru.

Hukumar zaben ta sanya sunan tsohon gwamnan jihar Ibrahim Shekarau a matsayin dan takarar sanatan Kano ta tsakiya din, a maimakon sunan Hanga da jam’iyyar ta turawa hukumar.
Da farko dai jam’iyyar ta NNPP ta bayar da sunan sanata mai ci shekarau a matsayin dan takarar ta na sanatan Kano ta tsakiya, wanda yaci zabe a jam’iyyar APC a zaben da ya gabata.

A baya Shekarau ya bar jam’iyyar APC zuwa NNPP inda ya zauna na dan wani lokaci, daga baya kuma ya fice ya koma jam’iyyar PDP sakamon rashin jituwa da suka samu da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP din Rabiu Kwankwaso.

Saidai INEC ta fitar da sunansa sakamakon cewa da tayi, ba’a sanar mata a hukumance kafin lokacin canjin sunan yan takara ya wuce ba bisa doka.
An jiyo sanata Shekarau yana bayyana cewa, INEC ta ki karbar takardar da ya kai mata na janye takara ne, sakamakon wa’adin da doka ta tanada na canja sunayen yan takara kafin zabe ya wuce.