An dakatar da shugaban Jamiyar APC a jihar Neija bisa zargin da zabar dan takarar jamiyar PDP Atiku Abukar a ranar zaben shugaban kasa da na yan majalissu a ranar Asabar.

Babban kwamiti na jihar karkashin jamiyar APC sun ce sun gano cewa shugaban jamiyar na yankin Agwara ya ci amanar jamiyar APC wato anti party.

Suka ce suna zargin Haliiru Zakari Jikantoro da yin amfani da kudin jamiyar APC domin taimakawa PDP a zaben da ya gabata.

Cikin kwamitin sun ce bisa karin wasu dalilai kamar kin neman yan jamiya a tattauna game da zabe lokacin da zaben yake tahowa ya nuna ba ya tare da APC, don haka sun dakatar da shi har zuwa yadda lokaci ya kama.

 

A wasikar da suka aike masa da ita a ranar biyu ga watan maris dauke da sahannun sakatarenta sun ce baya lura da abin da ya shafi APC kuma bisa wasu alamu shi ne wanda ya zabi dan takarar jamiyar PDP bayan ya fadi a akwatin zaben sa lokacin zabe.

Jamiayar PDP dai a matakin kasa ita ce wadda ta kasance a mataki na biyu a lokacin zaben shugaban kasa da aka fafata wadda tun lokacin da ake kawo kuri u na jihohi ta fara kalubalantar sakamakon,inda suke cewa busu yadda da wannan sakamakon da INEC ta bayyana ba.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: