Wasu guggum sojoji sun farma masu garkuwa da mutune tare da hallaka wasu daga ciki da kuma kubutar da mutane 14 a jihar kaduna.

Sojojin sun yi kai sumamen ne yayin da yan bindigar ke zaune a maboyar su a dajin karamar hukumar Chikun ta jihar kaduna.

Kamar yadda kwamishinan harkokin tsaron cikin gida samuel Arwan ya bayyana ya ce an samu nasarar ne sakamakon aiki da sojojin suka yi babu dare babu rana wajen tabbatar da tsaro a kaduna dama kasa baki daya.

Arwan ya ce an samu nasarar hallaka wasu daga cikin yan bindigar a dajin da kuma kubutar da mutane 14 inda aka samu maza tara da mata biyar a wajen yan bindigar.

Kuma ana ci gaba da bincike akan wadanda aka yi garkuwa da su 14 kafin daga bisani a mika su zuwa ga iyalan su domin ci gaba da rayuwa mai yanci.

Sannan ya ci gaba da cewa sojojin sun yi tarwatsa yan bindiga hadi da masaukin su dake dajin da samun mashina guda biyu da wasu kayayyakin amfani.

Sameul Arwan ya ce gwamna Malam Nasir Elrufai ya yabawa rundunar sojin Najeriya bisa irin kokarin da su ka yi da ma sauran jami an tsaro a Najeriya.

Malam ya ci gaba da cewa ba karammin aiki sojojin su ka yi bisa irin wannan aikin kwarewa da suka yi na kubutar da wadanda aka garkuwa da su a raye batare da wani rauni ba.

Sai dai wannan na zuwa bayan hallaka wani da ake zargin yan bindiga sun yi tare da garkuwa da akalla mutane 23 a garin kagarko a jihar ta kaduna a ranar Laraban data gabata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: