Wasu da ba san ko su wane ne ba sun kashe wani almajiri sannan suka kwakule idonsa a Jihar Jigawa.

An tsinci gawar ne bayan an jima ana neman shi, kafin daga bisa aka tsinci gawarsa kwance cikin jini an kwakule masa ido daya.
Rundunar ’yan sandan jihar ta ce kafin a gano gawar, malamin almajirin ya kai rahoto caji ofis cewa tun da yaron ya je neman ice ba a sake jin duriyarsa ba.

Kakakin rundunar, Lawal Shiisu, ya ce malamin mai suna Malam Muhammad Mustafa, ya yi musu korafi tun da misalin karfe 8 na safiyar Juma’a wani almajirinsa ya tafi nemo ice amma bai dawo gida ba.

Ya ce daga baya aka tsinci gawar almajirin an kwakule masa ido daya, aka kai shi Babban Asibitin Dutse inda likita ya tabbatar ya rasu.
A cewar Shiisu, rundunar ’yan sandan ta fara farautar wadanda suka yi wannan aika-aika.
Daily Trust
Ɗalibai mata 2 na jami’ar tarayya da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara, waɗanda suka shiga hannun masu garkuwa sun shaƙi isƙar ‘yanci.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa ɗaliban, Maryam da Zainab, sun kubuta daga hannun ‘yan bindiga bayan shafe kwanaki 12 a cikin Jeji.
Idan baku manta ba a baya an kawo rahoto cewa an sace daliban ne yayin da wasu yan bindiga suka kutsa gidan kwanansu a kauyen Sabon Gida.
Ƙungiyar ɗaliban jihar Zamfara ta tabbatar da dawowar daliban amma ba ta ce komai ba kan ko an biya kuɗin fansa kafin su kubuta.
Jami’in hulɗa da jama’a na ƙungiyar, Umar Abubakar, ya taya shugabannin jami’a murna da kuma iyayen ɗaliban, waɗanda Allah kaɗai ya san halin da suka shiga bayan sace ‘ya’yansu.
Wasu da ake zaton mayakan kungiyar Boko Haram ne sun kai sabon hari a jihar Yobe, inda suka kashe akalla mutum tara.
Channels TV ta ruwaito cewa lamarin ya afku ne a ranar Alhamis, 13 ga watan Afrilu a Buni Gari, karamar hukumar Gujba da ke jihar.
Mazauna garin Buni Gari, Baba Ibrahim da Iliya Maina sun sanar da Channels TV cewa al’ummar yankin sun shiga tashin hankali ne lokacin da wani mutum mai suna Shettima Dawi ya tafi neman itattuwa a yan kilomita kadan da garin amma bai dawo ba.
Lamarin ya sa yan uwan da makwabta haduwa don gano inda yake a cikin jeji, kawai sai mayakan Boko Haram suka farmake su.
Da aka tuntube shi, kakakin rundunar yan sandan jihar Yobe, Dungus Abdulkarim, ya tabbatar da harin.
DSP Abdulkarim, ya ce sabanin abun da rahotanni suka kawo, mutane tara yan ta’addan suka kashe.
Channels TV
Yan sanda sun kashe wasu mutum uku da ake zargin ’yan bindiga ne a Karamar Hukumar Lafiya ta Jihar Nasarawa.
An kashe wadanda ake zargin ne yayin wani artabu da suka da jami’an ‘yan sandan jihar a ranar Juma’a.
A yayin arangamar, an ceto wani mutum da suka sace mai suna, Ezekiel Luka – daga Jihar Taraba, sa’o’i 24 bayan sace shi.
Kakakin ‘yan sandan Jihar, Ramhan Nansel ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yammacin ranar Juma’a.
Nansel, ya ce jami’an ‘yan sandan sun samu bayanai a ranar Alhamis cewa wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun tare hanyar Assakio-Sabon Gida.
Ya ce a ranar 13 ga watan Afirlu 2023, an samu labarin cewa wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun tare hanyar Assakio-Sabon Gida da ke yankin Lafia, inda suka yi garkuwa da wani mutum mai suna Ezekiel Luka dan asalin Jihar Taraba.
Ya ce an kama wani da ake zargin dan bindiga ne da wata bindiga mai dauke da harsashi bakwai a cikinta.
Daily Trust
Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) a jihar Yobe ta ayyana Ibrahim Bomai a matsayin wanda ya lashe zaben sanatan mazabar Yobe ta Kudu a majalisar dattawa.
A cewar sakamakon zaben na yau Asabar 15 ga watan Afrilu, baturen zabe, Abatcha Melemi ya bayyana cewa, Bomai na APC ya samu kuri’u 69,596, inda ya lallasa abokin hamayyarsa na PDP, Halilu Mazagane da ya samu kuri’u 68,885.
Tun farko, hukumar zabe ta dakata da tattara sakamakon zaben yankin tare da ayyana shi a matsayin wamda bai kmamala ba, saboda wasu dalilai na aringizon kuri’u a rumfunan zaben Manawachi a karamar hukumar Fika.
Daga baya, an sanar da cikon zaben a yau Asabar don karasa zaben daga inda aka tsaya a watan Faburairun da ya gabata.
Da yake sanar da manema labarai sakamakon zaben, baturen zaben ya ce abin da ya fada gaskiya ne kuma shi ne adalci.
Tawagar kasar Argentina ta koma ta daya a kan jadawalin kasashen da ke kan gaba a buga kwallon kafa a duniya da FIFA ta sanar kuma wannan shi ne karo na farko da Argentina ta hau kan wannan matakin tun bayan shekara shida, wadda ta lashe kofin duniya a Kasar Katar a 2022.
Kasar ta Argentina ta samu wannan ci gaban bayan nasara biyu a wasan sada zumunta da ta ci Panama da Curacao, ita kuwa Brazil rashin nasara ta yi a hannun Morocco.
Faransa, wadda ta doke Netherlands da Jamhuriyar Ireland a wasannin neman shiga Euro 2024 ta koma ta biyu sai Brazil wadda take matakin farko ta koma ta uku, Ingila wadda ta ci Italiya da Ukraine tana ta biyar da Sifaniya a jerin ‘yan 10 farko.
Daga nan nahiyar Afirka kuma tawagar ‘yan wasan Super Eagles ta Nigeriya wadda Jose Pesseiro ke jan ragama ta yi kasa a jadawalin kungiyoyin da ke kan gaba a iya kwallo a duniya.
Najeriya wadda ta je ta ci Guinea Bissau 1-0 a watan jiya a wasan cikin rukuni a neman shiga kofin Afirka tana ta 40 a duniya, wadda take ta 35 a Disamba sannan a nahiyar Afirka kuwa Super Eagles wadda take ta biyar a baya yanzu Masar ta karbi gurbin, Najeriya ta yi kasa zuwa ta shida.
Ita ma Kamaru ta yi kasa daga mataki na hudu a baya yanzu tana ta bakwai a Afirka wanda hakan yake nufin akwai aiki sosai a gaban manya-manyan kasashen Afirka musamman masu tasiri a kwallon kafa.