Zababben Dan majalissar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Jalingo, Yorro da Zing a jihar Taraba Ismaila Yushau Maihanci ya rasu.

Maihanci ya rasu da safiyar yau Asabar, kuma za’a yi jana’izar sa bayan Sallahr Azahar a Masallacin Kasa da ke birnin tarayya Abuja.
Maihanci Dan shekaru 37 Dan kasuwa ne kuma Dan siyasa, an zabe shi Dan majalissar tarayya a zaben nan na shekarar 2023 da ya kammala karkashin tutar jam’iyyar PDP.

Kafin zabensa ya taba rike mukamin mai bada shawara na musamman ga gwamnan Taraba Darius Ishaku, sannan ya rike sakataren jam’iyyar PDP a jihar Taraba.

Ismaila Maihanci ya rasu ya bar mace guda daya wato Fatiha Sangari da kuma yaro namiji.