Rundunar yan sandan jihar Imo ta tabbatar da kama wasu mutane tara da ake zargin yan kungiyar aware ne ta Biyafara wato IPOB bayan hallaka jamian yan sanda biyar.

 

Da yake jawabi ga manema labarai kakakin rundunar yan sandan jihar Imo Henry Okoye shi ya yi holen matasan ga yan jaridu a jiya Litinin.

 

Henry ya ce mutanen an kama su daban daban inda aka kama babbansu a jihar Abia.

 

Sannan an kama sauran a Imo kuma sun tabbatar da sune suka hallaka jami’an yan sanda biyar a jihar Imo.

 

Kuma an kama su da muggan kayan laifi da dai sauran su, kuma sun bayyana cewa su yan kungiyar aware ta IPOB ne.

 

Sai dai kwamishinan yan sandan jihar ya yabawa jami’an jihar bisa irin wannan kokarin da suka yi kuma jama a su ci gaba da bada hadin kai tare da bayyana wata masaniya akan wadannan bata garin.

 

Kungiyar yan awaren Najeriya ta IPOB kungiya ce da ke neman ballewa daga kasar ta karfin da yaji domin kafa sabuwar kasa mai suna Biyafara,

 

Sai dai gwamnatin kasa Najeriya ta haramtawa duk mai burin shiga kungiyar.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: