Wasu da ake zargi ‘yan bindiga ne sun yi garkuwa da wani limamin wata coci mai suna Owu Ujo a ranar Juma’a a Jihar Imo.

 

Daraktan yada labaran Cocin da Limamin yake jagoranta shine ya tabbatar da faruwar lamarin.

 

Daraktan ya bayyana cewa ‘yan bindigan sun yi garkuwa da shi ne akan hanyar karamar hukumar Oguta da Mbaitoli a Jihar.

 

Maharan sun yi garkuwa da shi ne a lokacin da yake dawowa zuwa Owerri daga gurin bikin binne gawar mahaifin wani fasto abokinsa a Izambe cikin karamar hukumar ta Oguta.

 

Wata majiya ta bayyana cewa ‘yan bindigan sun yi garkuwa da shi tare da wadanda su ke cikin motar tashi.

 

Sai dai ba mu samu tabbaci daga jami’an yan sandan jihar ba hau zuwa lokacin da mu ke kawo muku wannan labari.

Leave a Reply

%d bloggers like this: