Gungun magoya bayan jam’iyyar NNPP sun yi wa sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero Ihu, a filin wasa na Sani Abacha wurin da ake bikin rantsar da sabon gwamna.

Dirar sarkin ke da wuya wajen taron, wasu fusatattun matasa su ka fara yin ihu da muryoyinsu cikin kuwwa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa sarkin Bichi Alhaji Nasir Ado Bayero, wanda kani ne ga sarkin na Kano shima ya samu irin wannan tarbar a wajen taron.

Saidai jami’an tsaro sun yi saurin shiga tsakani, inda su ka raka sarakunan zuwa wuraren zamansu.

Yau Litinin ne dai 29 ga watan Mayun shekara ta 2023 ake bikin rantsar da sabon gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP, kuma sarakunan sun samu takardar gayyata zuwa wajen bikin rantsuwar a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano.

Leave a Reply

%d bloggers like this: