Wata kungiya mai zaman kanta ta buƙaci hukumar dake dakile masu yiwa tattalin arzikin kasa ta’anati EFCC da ta fara bincike akan faifan bidiyon da ake zargin an ga tsohon gwamnan jihar Kano ya na karbar cin hanci.

 

Kungiyar ta bayyana haka ne a wata takarda da ta rabawa manema labarai a jiya Laraba.

 

Ƙungiyar karkashin shugabanta Kwamared Umar Ibrahim Umar, sun buƙaci bincike tare da gano sahihin bayani a dangane da zargin.

 

Ta ce tun a wancan lokaci shekarar 2018 ne aka dakatar da majalissar dokokin jihar Kano daga binciken Ganduje akan karbar kudin bayan umarnin kotu.

 

Sai dai kungiyar ta ce yanzu Ganduje ya cire wannan riga don haka a bincike shi.

 

Ta ci gaba da cewa kiran harda hukumar ICPC mai hana rashawa su hadu guri guda da su tabbatar sun yi bincike akan Ganduje.

 

Ta ce bincike akan Ganduje shi ne zai sa duk wanda yake da mugun Abu ya sha jinin jikinsa kuma ya daina karɓar rashawa.

 

A shekarar 2018 ne jaridar Daily Najeriya ta saki wani faifan bidiyon da aka ga tsohon gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje yana karbar kudade ya na jefawa a aljihu.

 

Abin da ya sanya Alumma cikin tsammani hakan ta tabbata ko bai tabbata ba.

 

Sannan majalissar dokokin jihar Kano ta fara bincike akan faifan bidiyon sai dai kotu ta dakatar saboda akwai rigar kariya a jikinsa.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: