Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a jihar Kogi sun bayyana cewa za su koma don kara yin garkuwa da wasu mutanen.

 

Mutanen sun yi garkuwa da wasu mutane Uku a ranar Litinin din da ta gabata a yankin Greenland dake karamar hukumar Ajaokuta a jihar Kogi.

 

Kamar yadda wani shaida ya bayyana tare da kin fadin sunansa.

 

ya ce yan bindigar sun shiga garin na Greenland tare da harbin mutane yayin da suke lamuransu .

 

Kuma kamar yadda bayanai su ka nuna, yan bindigar sun shiga ne su ka dauki wani mutum wanda tsahon ma’aiakacin tsaro ne.

 

Shi ma shugaban karamar hukumar ta Ajaokuta ya tabbatar da lamarin inda ya ce mutanen garin suna zillimi dukda gwamnati na iya kokarinta a ciki.

 

Wani mutum wanda daya ne daga cikin ahalin wadanda aka yi garkuwa da su, ya bayyana cewa yan bindigar sun kirawo su tare da neman kudin fansa a gurinsu dukda bai bayyana nawa aka nema ba.

 

Sannan suka ce za su dawo don kara yin garkuwa da wasu mutanen a garin.

 

Sai dai jaridar Punch ta tuntubi yan sandan Jihar Kogin Amma sun ce za su yiwa yan jaridu bayani daga baya.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: