Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta rufe wani kamfanin ‘yan China bisa zargin wulakanta ma’aikanta ‘yan Najeriya.

Kamfanin mai suna Shaanxi Construction Engineering Group Corporation ana zarginsa da cin zarafin ma’aikatansa.


Kungiyar ta isa harabar kamfanin da ke kusa da sabuwar Hedkwatar ECOWAS a Lugbe da misalin karfe 7:30 na safe.
Daily Trust ta kawo rahoton cewa da farko an hana kungiyar shiga cikin kamfanin saboda an kulle mashigar, amma daga bisani sun samu damar shiga.
Hukumomin kamfanin ba su ce komai ba kuma ba su mai da martani game da korafe-korafen kungiyar ba.
Gwamnatin kasar China ce ta dauki nauyin gina sabuwar sakatariyar ECOWAS din don kyautata wa mazauna yankin da taimakon su.
Sakataren kungiyar, Emmanuel Ugboaja ya koka kan yadda kamfanin ke wulakanta ma’aikanta akan aiki.