Gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf, ya ba da hujjarsa ta aikin rusa gine-gine da gwamnatinsa ta fara tun bayan hawansa karagar mulki a ranar 29 ga watan Mayu, Channels Tv ta ruwaito.

Da yake tabbatar da kudurin gwamnatinsa na gudanar da aikin yayin bikin Sallah, Gwamna Yusuf ya bayyana cewa yana aikin rusau ne domin kwato kadarorin jama’a kuma mallakin gwamnati.


Wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Hisham Habib ya fitar, ta ce Gwamna Yusuf ya jaddada muhimmancin kwato kadarorin gwamnati da wasu daidaikun mutane da shafaffu da mai a gwamnatin Ganduje suka mallaka ba bisa ka’ida ba.
Da yake jawabi ga mai martaba a ya yin gai suwar sallah ya ce.
Mai martaba, yana da kyau majalisar masarauta ta lura cewa sun fara aikin rusau ne domin kwato kadarorin gwamnati da aka mallakarwa wasu ba bisa ka’ida ba, kuma za su tabbatar da cewa an dawo da duk wadannan kadarorin domin amfanin mutanen Kano.
Gwamnan ya nuna jin dadinsa ga mai martaba sarkin da majalisar masarautun Kano bisa ziyarar da suka kai masa, inda ya bayyana cewa wannan ita ce ziyara ta farko da ya samu tun bayan hawansa mulki.
Ya yi amfani da damar wajen bayyana nasarori da dama da gwamnatinsa ta samu a cikin kwanaki 31 da suka gabata.
Tun bayan hawan Abba Gida-Gida ake ci gaba da cece-kuce da maganganun ra’ayoyi kan rusau da yake yawan yi a Kano.