Kungiyar IPMAN ta ‘yan kasuwan mai sun yi watsi da jita-jitar da ke yawo a kan batun karin kudin litar man fetur daga kusan N500 a yau.

 

Vanguard ta ce kungiyar ta yi karin bayanin ne a ranar jama’a, ta na mai ba mutane shawarar su daina sayen fetur su boye saboda tsoron tashin farashi.

 

Shugaban IPMAN na reshen Kudu maso yamma, Alhaji Dele Tajudeen ya bayyana haka jiya a garin Ibadan da ke jihar Oyo, ya na musanya rade-radin.

 

“Ya ce yana so ya ankarar da mutane su daina tada hankalinsu a kai, babu dalilin shiga cikin firgici, su na kan batun, kuma babu wani abin da ke kama da haka.

 

Idan a ka duba farashin da ke hannun NNPCL, sun fi manyan ‘yan kasuwa damar samun riba.

 

Saboda haka farashin saidawar su ne su ka sanar, ba su taba tsaida farashi ga ‘yan kasuwa ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: