Masu sharhi kan harkokin siyasa na ciki da wajen Nijeriya sun karkata kan majalisar ministocin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai kafa.

An dai ayyana Shugaba Tinubu a matsayin shugaban Nijeriya ne bayan ya lashe zaben da aka gudanar a watan Fabrairu wanda a halin yanzu ake kalubalantarsa a kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa da dan takarar jam’iyyar PDP, tsohon mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar da kuma dan takarar jam’iyyar LP, Mista Peter Obi.
An ci gaba da ce-ce-ku-ce kan shugabancin Tinubu kan yadda ‘yan Nijeriya ke fatan ganin wa’adin mulkinsa ya kai ga cigaban al’ummar kasar bayan da ya cimma burinsa na shugaban kasar Nijeriya.

Tuni dai Shugaba Tinubu ya dauki kwararan matakai dangane da maye gurbin shugabannin hukumomin tsaro da dakatarwar da ya yi wa gwamnan babban bankin kasa, Godwin Emefiele da kuma na shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa, amma har yanzu ‘yan Nijeriya da dama na cikin kokwanton kan abubuwan da suke tsammani ga Shugaba Tinubu.

A wurin bikin rantsuwa na ranar 29 ga watan Mayun 2023, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa shi mai cin gajiyar goyon baya ne da kuma fatan na gari ga al’ummar Nijeriya, inda ya yi alkawarin ba zai ci amanar miliyoyin ‘yan Nijeriya ba.