Akalla mutane 36 aka kashe cikin makonni biyu a jihar Borno.

Rahotanni na nuni da cewa an hallaka mutanen ne a wasu hare hare hudu da aka kai jihar.
Sai dai mafi yawa daga cikin mutanen da aka kashe manoma ne da aka rutsa su su na tsaka da aiki a cikin gonakinsu.

An kashe mutanen a tsakanin ranar 14 ga watan Yuni zuwa ranar 30 ga watan Yuni wanda ya yi sanadiyyar samun raunin wasu manoman.

A sakamakon hare haren da aka kai musu ya sa manoma da yawa kauracewa zuwa gonakinsu a daminar bana.
Sai dai hare haren da aka kai an fi kaiwa shiyyar Borno ta Arewa wanda nan ne cibiyar noma.
Masana na alakanta yankin da cibiyar samar da abinci sai dai hakan na barazana ga noma a bana sanadin kauracewa gonakin da manoman ke yi.
