Gwamnatocin sojin kasashen Burkina Faso da Mali sun aike da jirgin yaki Jamhuriyar Nijar domin taimaka mata akan yunkuri da ECOWAS ke yi na aike da sojinta domin kwatar mulki daga Kasar.

Jaridar Daily trust ta rawaito cewa gidan talabijin gwamnatin Nijar ne ya tabbatar da aiko da jiragen daga Burkina Faso da Mali a ranar Juma’a, inda aka ajiye jiragen akan iyakokin Kasar ta Nijar.

Bayan aikewa da Jamhuriyyar ta Nijar jiragen gwamnatin sojin ta Nijar ta bayyana jin dadinta da haɗin kan da ƙasashen biyu su ka ba ta.

Inda ta ce sun cika alkawarin da suka ɗauka bisa ajiye jiragen yaƙinsu domin yakar masu shirin kai hari Jamhuriyyar.

Kasashen biyu sun aike da jiragen yakin ne domin taimaka wa Jamhuriyar ta Nijar ta yaki matakin yin amfani da karfin soja da kungiyar ECOWAS ke shirin yi a ƙasar.

Gwamnatin sojin Nijar ta bayyana aniyar ta na fara ɗaukar jami’an sa-kai a ranar Asabar, a shirinta na yakar sojin ECOWAS, bisa yunkurinsu na dawo da mulkin dimokuradiyya a Kasar.

Sojin za su dauki matasa ne wadanda ba su wuce shekara 18 ba a duniya.

Gwamnatin ta Nijar za ta fara tantance matasan ne a filin wasa na Janar Seyni Kountche da ke Yamai, daga bisani a tantance wasu akan iyakokin kasar na Jamhuriyar Benin da Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: