Rundunar yan sanda a jihar Gombe ta ƙaddamar da shiri domin tabbatar da rufe dukkanin gidajen Gala a jihar.
Hakna ya biyo bayna umarnin gwamnan jihar na rufe dukkanin gidajen gala a jihar.

Kwamishinan yan sandan jihar Oqua Etim ne ya tabbatar da ɗaukar mataki don ganin an rufe dukkanin gidajen a jihar bisa umarnin gwamnan jihar.

A waata sanarwa da mai magana da yawun ƴan sandan jihar ASP Mahid Muazu Abubakar ya sanyawa hannu a yau, ya ce kwamishinan ya buƙaci masu gidajen da su tabbata sun yi biyayya ga umarnin gwamnatin.

Sanarwar ta ce ƴan sanda haɗin gwiwa da sauran jami’an tsaro za su tabbatar da cewar an rufe kowanne gidan gala a jihar.

Sannan a shirye su ke domin hukunta duk wanda ya ƙi bin dokar da gwamnatin jihar ta sanya.

Gwamnan jihar ne dai ya bayar da umarnin rufe dukkanin gidajen gala a jihar, kuma ake zargi umarnin daa alaƙa da wani bidiyon baɗala da ke yawo a kafofin sa da zumunta wanda aka yi a guda cikin gidajen gala na jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: