Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta bukaci daukacin al’ummar Najeriya da su shiga cikin “gangamin neman yanci”, inda ta dage cewa za ta shiga yajin aikin sai baba ta gani daga ranar Talata.

 

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar NLC, Joe Ajaero, ya fitar a safiyar ranar Lahadi, 1 Oktoba, na bikin cikar kasar shekaru 63 da samun ‘yancin kai.

 

Ya sanar da yan Najeriya cewa za su cimma nasara idan suka tsaya tsayin daka a matsayin kungiya da ba za a iya raba kanta ba.

 

Kungiyar kwadago ta yi kira na musamman ga yan Najeriya yayin da take shirin fara yajin aiki.

 

Ajaero ya bukaci dukkan masu masu fada aji a kasar, musamman masu rike da sarautun gargajiya da su roki gwamnati ta sauke nauyin da ke kan jama’a.

 

Shugaban kungiyar kwadagon ya bukaci yan kasar da su yi bikin ranar ‘yancin kai tare da sabunta manufarsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: