Kimanin sojojin Isra’ila 169 aka kashe a rikicinsu da kungiyar Musulunci ta Hamas da ke ƙasar Falasɗin, bayan sojojinta sun Ƙaddamar da hari akan iyakokin ƙasar.

Mai magana da yawun rundunar sojin Daniel Hagari ne ya sanar da hakan ga manema labarai, a safiyar yau Laraba.

Hagari ya ce “da safiyar nan mun sanar da iyalan sojojinmu guda 169 da aka kashe, kuma mun sanar da iyalan sojojin guda 60 da aka sace zuwa Gaza a wannan rikicin”

Ya ce kuma babu wani sabon kutse da suka samu labari daga sojojin Gaza tsawon kwanaki biyu, amman akwai ɗaruruwan gawarwakin ƴan Bindiga da ba a kawar da su ba har yanzu akan iyakar.

Hagari ya ƙara da cewa “suna da niyyar ƙwace yankin ne, ba wai sun tsara yin mamaya bane da nufin komawa Gaza daga baya”

Isra’ila dai tana fama biyo bayan harin da Ƙungiyar Hamas ta Ƙaddamar a kanta ranar Asabar ɗin da ta gabata, wanda aka tabbatar da mutuwar kimanin mutane 1, 200.

Yayin da a yankin Gaza kuma mutane 1,055 suka rasa rayukansu, sakamakon harin mayar da martani da ƙasar Isra’ila ta yi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: