Rundunar ƴan sandan jihar Neja ta damƙe wata matashiya mai shekaru 14 mai suna Joy Afekafe.

Ana zargin ta ne dai da kitsa kashe wata malamar jami’a mai suna Funmilola Sherifat, wacce ke aiki a jami’ar fasaha ta gwamnatin tarayya da ke Minna a jihar Neja.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda aka yiwa mamaciyar yankan rago, a gidanta da ke yankin Gbaiko cikin birnin Minna, a ranar Asabar da ta gabata.

Wacce ake zargin ta kasance ƴar aikin gidan marigayiyar malamar jami’ar, an ruwaito cewa ta ja da baya daga yin aikin kwanaki biyu kafin a kashe marigayiyar.

Yayin gabatar da wacce aka zargin, Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Neja Wasiu Abiodin ya ce, Joy Afekafe ita ce babbar wacce aka zargi a’a aikata laifin.
Ya ce sun yi bincike ta hanyar tattaunawa da maƙota, ƴan da abokai a yankin, kuma bincike ya kai su ga damƙe mai aikin gidan mamaciyar, wato Joy Afekafe mai shekaru 14.
Ya ce yayin da su ke wa wacce aka zargin tambayoyi, ta amsa cewa tayi aiki a gidan marigayiyar na tsawon makonni uku, sai dai ta bar aiki saboda ɗabi’unta a gidan, bayan ta tafi ta haɗu da abokiyar karatun ta, wacce su ka kitsa yadda za su farmaki gidan malamiar jami’ar.
Wasiu ya ce, Joy ta gaya musu cewa ta ɗauki abokanta maza mutum biyu zuwa gidan, ranar 28 ga watan Oktoban da ƙarfe 4:00 na yamma a kan babur.