Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce, dukkanin wasu jami’an gwamnati da masu riƙe da muƙaman siyasa idan ba zasu iya aikin da aka basu ba to su sauka.

Yayin da yake bayyana haka ya ayyana cewa, ko ta halin ƙaƙa dole sai gwamnatinsa ta yi nasara, don cimma muradan ƴan Najeriyar da su ka zaɓe shi.

Ya bayyana hakan ne a yau Laraba, wajen wani taron kwanki uku da aka shirya. Don bayyana ƙudurinsa na kyakkyawan fata da sabunta buri da jami’an gwamnatinsa su ka shirya a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Yayin da yake jawabi ga mahalarta taron Tinubu ya ce, duk wanda zai yi aiki kar ya ji wani tsoro, wanda ba zai yi ba ma zasu gani, idan mutum ba zai iya ba kuma to kawai ya tafi.

Shugaba Tinubu kuma ya tabbatar musu da cewa zai tsame hannunsa a ayyukansu don basu damar yi yadda ya dace, kuma ya basu shawara da su yi tambaya akan yadda zasu yi da kuma yaushe za su gudanar da aikin nasu.

Ya kuma ƙara kira ga ministocinsa da muƙarraban gwamnatin, da su taimaka masa don ganin an samu nasara a tafiyar.

Ya ƙara da cewa a matsayinsa na ɗan Adam zai iya yin kuskure, kuma in dai an nuna masa kuskuren nasa to zai yi saurin gyarawa.

Ya kuma jaddada cewa shi shugaba ne ga dukkan ƴan Najeriya, ko suna da ra’ayin siyasa ko basu da shi, ƙasa kamar gidan iyali ne babba guda ɗaya, da mutane daban-daban a kowanne ɗaki.

A Ƙarshe ya tabbatar wa da masu saka hannun jari na ƙasashen ƙetare, basu dama don su zo su baza hajar su, su saka hannun jari su samu ribarsu ba tare da kowacce matsala ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: