Fiye da mutane 24 ne su ka mutu a wani yanayi mai kama da dawowar kai harin ƴan ƙungiyar Boko Haram, a ƙauyen Nguru Kayayya da ke ƙaramar hukumar Geidam ta jihar Yobe.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa maharan sun kai hari ga al’ummar yankin, sun kuma kashe mutane huɗu ciki har da dagacin garin, sun kuma ƙona gidaje da yawa.

Ba tare da sanin al’ummar ƙauyen ba, ƴan ta’addar sun dasa abin fashewa a yankin, bayan ya fashe ne ya hallaka mutane 20 waɗanda su ke wasu akan babura da ake kiransa da JEGA. Yayin da suka kai ziyara ga mai garin washe garin ranar da aka kai harin farko a yankin.

Wani shaidar gani da ido da ya buƙaci a ɓoye sunansa saboda dalilin tsaro ya ce, mutane biyu ne kacal su ka tsira bayan tarwatsewar abin fashewar.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Yoben Dungus Abdulkarim, ya tabbatar da afkuwar lamarin amman bai bayar da cikakken bayani ba.

Wata mai jiya mai tushe da ta zanta da jaridar Premium Times ta ɓoyayyiyar siffa, ta tabbatar da cewa harin na ramuwar gayya ne.

Wani shaida mai suna Aujara Idris ya ce, ƴan ta’addar sun kawo harin ne sakamakon mutanen garin sun ƙi biyan haraji ga ƴan ta’addar, harajin da su ke karɓa daga wajen su akan gonakinsu ko Gidajensu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: