Yan sanda a jihar Katsina sun yi nasarar kama kimanin mutane 134 da ake zargi da aikata manyan laifuka daban-daban a jihar cikin watan Oktoba da ya gabata.

Kwamishinan yan sandan jihar, Aliyu Abubakar Musa, ne ya bayyana haka a yayin da yake yiwa manema labarai karin haske a ranar Laraba a Katsina.
Abubakar Musa wanda ya yi bayanin ta hannun mai magana da yawun yan sandan jihar ta Katsina, ASP Abubakar Aliyu, ya ce wadanda ake zargin an kamasu bisa zargin fashi da makami, garkuwa da mutane, satar shanu, da kuma kisan kai.

A cewar kwamishinan, wasu daga cikin wadanda ake zargin kuwa ana tuhumarsu ne da zargin aikata fede, da safarar miyagun kwayoyi, da kulla alaka da kungiyoyin yan ta’adda da dai sauransu.

Masu laifuka 72 cikin 75 na laifukan da aka sanar da yan sanda an mika su ga kotuna domin sauraro da yin hukunci.
Kwamishinan ya kara da cewa mutane 23 da aka yi garkuwa an samu nasarar kubutar da su a cikin watan na Oktoba, yayin da aka kwato bindigo kirar Pistol, da harsashi guda 6, da mota da kuma sauran kayayyaki.
Daga karshe kwamishinan yayi kira ga al’umma da su cigaba da bawa yan sanda da sauran hukumomin tsaro hadin kai tare da bayar da bayanai da za su cigaba da bada damar kama masu laifuka a fadin jihar.