Tsohon ministan sadarwa Adebayo Shittu ya ce, tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ba ya tambayar ministocinsa yadda su ke gudanar da ayyukansu.

Shittu yana tsokaci ne game da halartar taron ministocin shugaba Tinubu, yayin wata zantawarsa cikin shirin “Siyasa A Yau” na gidan talabijin na Channels.
Shittu ya ce “Buhari bai taɓa yin barazana ga kowa ba, kamar yadda na faɗa, Buhari ba kamar Tinubu bane, kuma Tinubu ba kamar Buhari bane.”

“Abinda na sani akan Buhari tare da dukkan girmamawa a gare shi, shi mutum ne wanda ba ruwansa, idan ya bai wa mutum aiki, ba zai taɓa tambayar mutum ya wannan aikin yake tafiya ba.”

“ya kamata na faɗi wannan ko dan amfanar ƙasa, don haka duk wanda ya zo bayan shi sai ya yi abinda ya kamata.”
Shittu ya ƙara da cewa, a yayin zamanin mulkin Buhari, idan ba ka je ka same shi ba shi ba zai taɓa tambayarka ba, ko da kuwa zai kai tsawon shekaru huɗu.
A Ƙarshe Shittu ya ce, cikin jawabin Tinubu na yau, ya nuna himmarsa na yin abu na daban, abinda nake ganin ya kamata ya ƙara shi ne, ya jagoranci yin abu a buɗe da sanya ido akan kowacce ma’aikata.