Babbar kotun jihar Rivers ta dakatar da majalisar dokokin jihar da kakakin majalisar, Martin Amaewhule kan yunkurinsu na tsige gwamnan jihar Siminalaye Fubara.

Haka zalika kotun ta dakatar da mataimakin kakakin majalisar dokokin, da babban joji na jihar kan bukatarsu ta tsige gwamnan.

Mai shari’a, Ben Whyte, ya yanke hukuncin ne biyo bayan karar da babban lauyan gwamnan, Damian Okoro, ya shigar a madadin gwamnan.

Har ila yau, mai shari’an ya bada umarnin cewa wajibi ne kowane bangare su girmama hukuncin kotun tare da kiyaye doka.

Gwamnan jihar ta Rivers dai na cigaba da fuskantar kalubale daga majalisun jihar inda su ke kokarin tsigeshi daga kujerarsa, sai dai zuwa yanzu gwamnan ya samu wata garkuwa daga kotu inda ta dakatar da tsigeshi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: