Rundunar sojojin Najeriya tare da ƴan sa kai sun samu nasarar ceto wasu mutune huɗu da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su a tsaunin Bangi da ke a ƙaramar hukumar Suru a jihar Kebbi.

Sojojin da suka fito daga bataliya ta Ɗaya, ta rundunar sojojin Najeriya, a Birnin Kebbi, sun kuma fatattaki ƴan ta’adda da dama a yaƙin da suke yi da masu tayar da ƙayar baya.

Daraktan tsaro na ofishin majalisar zartarwar jihar Kebbi, Abdulrahman Usman ne ya bayyana haka ga manema labarai a Birnin Kebbi a daren ranar Laraba, 1 ga watan Nuwamban 2023.

Ya bayyana cewa mutane huɗu da aka ceto sune, Malam Audu Fulani mai shekara 45, Umaru Wakili mai shekara 14, Alhaji Imam mai shekara 50 da kuma Chaggo Garba mai shekara 19.

Usman ya tabbatar da cewa jami’an tsaro na samun nasara kan ƴan ta’adda a jihar tun daga lokacin da Gwamna Nasir Idris Kauran Gwandu ya ba su umarnin murƙushe su da ƙarin kayan aiki.

Ya kuma yabawa gwamnan bisa goyon bayan da yake baiwa jami’an tsaro bisa kokarin da suke yi na kawo ƙarshen matsalolin tsaro a jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: