Shugaban Ma’aikatan jihar Kano Alhaji Usman Bala ya yi murabus daga kan mukaminsa.

Sanarwar hakan na kunshe ne cikin wani sako da Sakataren Gwamnatin Kano, Dokta Abdullahi Baffa Bichi ya sanar a ranar Laraba.
Sanarwar ta ci gaba da cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya umarci babbar sakatariyar hukumar ma’aikatan, Hajiya Ma’azatu Isa Dutse ta ci gaba da lura da ayyukan Ofishin har zuwa lokacin da za a nada sabon shugaban ma’aikatan.

Tun a watan Afrilun 2022 ne tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya naɗa Alhaji Usman Bala a matsayin Shugaban Ma’aikatan na Kano.

Bayan wata guda da yi masa naɗin, Ganduje ya sake daga likafar Alhaji Bala, inda ya kara masa da mukamin Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Kano.