Kungiyar kare hakkokin tattalin arziki da bin diddigin ayyuka (SERAP) ta roki Bankin Duniya da ya dakatar da ba jihohin Najeriya rancen kudi.

A cewar SERAP, ta na zargin jihohi 36 na Najeriya da almubazzarancin kudaden jama’a, wanda zai iya hadawa da kudaden da suke karba daga bankin.

A wata wasika mai kwanan wata 25 ga watan Nuwamba 2023, kungiyar ta nemi shugaban bankin, Ajay Banga, ya gudanar da bincike kan basussukan da aka ba jihohin.

Kungiyar ta ce idan har an samu johohin da aikata laifin almundahana da almubazzaranci, to bankin ya hana johohin rancen kudi kwata-kwata.

Ta kuma bukaci bankin ya dakatar da bayar da damar karbar bashi ga jihohi 36 har sai jihohin sun yi bayanin yadda suka kashe kudaden da suke karba daga bankin.

Manema labarai sun ruwaito cewa hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mataimakin daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare ya fitar a ranar Lahadi.

SERAP ta yi nuni da cewa bashin da ake bin jihohi 36 hadi da babban birnin tarayya ya kai naira tiriliyan 9.17, yayin da ake bin gwamnatin tarayya bashin naira tiriliyan 78.2.

Leave a Reply

%d bloggers like this: