Majalisar zartawa a Najeriya ta amince da kashe Naira tiriliyan 27.5 a matsayin kasafin kudin shekarar 2024, wanda shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu zai gabatar a zauren majalisa a gobe Laraba.

Ministan kasafi da tsare tsare na kasa Atiku Bagudu shi ne ya bayyana haka, jim kaɗan bayan zaman majalisar zartarwa da ya gudana a fadar shugaban ƙasa ranar Litinin.

Ya ce an samu ƙarin Naira tiriliyan 1.5 la’akari da kasafin shekarar da za ta gushe.

Daga cikin sauye-sauyen da aka samu har da amincewar karyar da Dalar Amurka, wadda a yanzu a hukumance ake siyar da dala ɗaya a kan Naira  750 maimakon Naira 700 da ake siyarwa a baya. Sannan kasafin ya dubi hawan farashin gangar mai a kasuwar duniya.

A gobe Laraba ake sa ran shugaban zai gabatar da kasafin kuɗin a gaban majalisa, domin neman sahalewarta don ha zama doka.

Karo na farko kenan da shugaban zai gabatar da kasafi a zauren majalisar, tun bayan kasancewarsa shugaban kasar Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: